Fatalwa

Daga Wiktionary

Hausa[gyarawa]

Fatalwa wata irin siffa mai kama da aljana wanda take shiga kurwar mamaci ta fito ta ba wanda ya taɓa cutar ta tsoro. Fatalwa a cikin mafarki suna da launi da motsi. Suna haifar da fargaba, tsoro, fushi ko wasu motsin rai. Al'ada Hausawa sun yi imani da samuwar fatalwa da kuma ire-iren ayyukanta na ban tsoro da firgitawa. Ita ma fatalwa wajen bahaushe ba iska ba ce, ba gunki ba ce, ba kuma dabba ba ce ba kuma mutum ce ta haƙiƙa ba. Fatalwa ƙirƙirarren wani abu ne da bahaushe ya ƙirƙiro domin kara wa imaninsa kayan aiki kawai. siffar fatalwa Bahaushe na bawa fatalwa siffar mutane na zati. Domin Bahaushe cewa ya yi fatalwa kasusuwan mutum ne gabadaya ba tare da fata ko tsoka ba ko jijiya ko daya ba. za a iya gane zatin mutum daidai tsayinsa da yawansa, yana kuma tafiya amma ba ya magana da kowa. Idan Bahaushe ya ga mutum ya rame sosai saboda yunwa ko rashin lafiya yakan ce, “wane ya koma kashi zalla kamar fatalwa” wannan ya tabbatar da siffara da Bahaushe ke siffanta fatalwa da ita na zama kassa zalla ba tsoka.