dalla

Daga Wiktionary

Hausa[gyarawa]

Bayani[gyarawa]

dalla raga ce wacce ake yinta da zare, ana amfani da ita ne ta hanyar riƙe gefe da gefenta, sai mutane su ratsa cikin ruwan suna ja. Duk kifin da suka tokare shi to ba zai iya wucewa ba. Can zuwa wani lokaci sai su nannaɗe ta da kifayen a ciki su fita da ita wajen ruwa sai su ciccire kifin.

Misali[gyarawa]

  • Dalla ta ta huje.
  • Ina amfana da wannan dalla gaskiya
  • Dallar yanzu bata da ƙarko