koma
Appearance
Hausa
[gyarawa]Bayani
[gyarawa]Koma jaka ce ta raga-raga da ake yiwa baki mai girma. Linki biyu ake yinta. Ana riƙe kowace ɗaya da hannu ɗaya. Wato ɗaya a dama ɗaya kuma a hagu. Idan aka shiga ruwa da ita sai a riƙa tafiya, can kuma sai a haɗe bakin a fitar waje.
Misali
[gyarawa]- Nasiyo babbar koma.
- Jiya Alhaji yabani Aron komar shi.
- Koma yanzu tayi kuɗi sosai.