Allah

Daga Wiktionary
Jump to navigation Jump to search

Karin magana[gyarawa]

Wanda bai godiyar mutane bai gode Allah> In Allah Ya soka kowa ma ya kika>

Allah maganin komai.

Allah mai mutane, wait jaba ta ga dogon bakin mijinta.

Allah na taimakon wanda ya taimaki kansa.

Babu nesa ga Allah.

Bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abinci.

In Allah ya taimake ka, kai kuma ka taimaki na baya gare ka.

Sai an sha wuya a kan tuna Allah.

Wanda bai gode wa Allah ba, ya gode wa azabarsa.

Allah guda gari bamban.

Allah maisa wa tuwon makaho mai.

Allah wadaran naka ya lalace, karan dawa da yaga na gida.

Allah ka fidda A'i ga rogo.misali shafiupac ya je jarabawa (gwadi) sai wani yace to Allah Ya fidda A'i ga rogo nufin cewa an dai sha wuya to Allah Yasa yau a samu sa'a.

Allah sarki barawo hannun mata: wato ita wannan magana tana nufin in dai kamu sun kama amma kam zai sha kashi.