aboki
Hausa[gyarawa]
Aboki Aboki (help·info) Shine wanda ake tare da shi a wami al'amari. abokai, ƙawaye ƙawa,
Noun[gyarawa]
àbōkī (n.) àbōkìyā, àbuyà (t.) (j. àbōkai, àbōkànai)[1]
Derived terms[gyarawa]
Translations[gyarawa]
- Faransanci: ami n.
- Harshen Malai: kawan
- Harshen Portugal: amigo, amiga
- Inyamuranci: enyi
- Ispaniyanci: amigo, amiga
- Italiyanci: amico n.
- Jamusanci: Freund n.
- Larabci: صَدِيق (ṣadīq, n.), صَدِيقَة (ṣadīqa, t.), صَاحِب (ṣāḥib, n.), صَاحِبَة (ṣāḥiba, t.)
- Setswana: tsala, j. ditsala
- Turanci: friend[2]
- Yarbanci: ore.
Karin magana[gyarawa]
- Abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa.
- Abokin damo guza.
- Abokin gamin maɗi, garin tamba.
- Abokin gamin masa sure.
- Abokin kiyayi zaman zauri, ka san gussuri, ka ba hauri, gida ba samu komi ba.
- Abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa.
- Abokin lalataci, lalatace.
- Abokin sarki sarki ne.
- Mai koraka shi ne abokin mai ƙi wuya.
- Maraki ba abokin tafiya ba ne.
- Matsiyaci abokin sarki.
- Talaka ba aboki, ko ka so shi, ran buki ka ƙi shi.