Riga

Daga Wiktionary
Jump to navigation Jump to search

Riga kalmar riga tana nufin nau'in tufafi da mutum ke sanyawa domin rufe tsiraici tsakanin wuya zuwa cibiya amma tana iya zarcewa har zuwa guiwa ko fiye da hakan. A wasu wuraren akan kiranta da taguwa. Riga a ma'ana ta biyu, na nufin amfani da wani kwano ko kwarya tare da samun ruwa wajen tace tsakuwa daga cikin hatsi, kamar shinkafa gero da dawa.[1]

Suna jam'i. Riguna

Misalai[gyarawa]

  • Yaro yasanya sabuwar riga.
  • Tela ya ɗinka riga.

Karin Magana[gyarawa]

  • Wanda zai baka riga to kaduba ta wuyansa.