Jump to content

Zomo

Daga Wiktionary
zomo

Zomo About this soundZomo Rabbit  Dabba ne mai rayuwa yawanci a daji yana da kuma dogayen kunnuwa kuma yana da masifar gudu kuma mafi akasari suna gina rami ne nanne gidan su. [1]

Misalai

[gyarawa]
  • Wasu mafarauta sun kama zomo

Karin magana

[gyarawa]
  • Karen bana shi ke maganin zomon bana.
  • Sarautar Allah kare a bakin zomo.
  • Zomo ba ya kamuwa daga zaune.
  • Banza ba ta kai zomo kasuwa.
  • Ba ni na kashe zomon ba, rataya aka ba ni.
  • Zomo baya hushi da makashinsa, sai dai maratayinsa.
  • Kowa ya ci zomo ya ci gudu.

Manazarta

[gyarawa]
  1. Skinner, Niel (1965). Kamus Na Turanci Da Hausa (in Hausa/English). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd. pp. 3–7. ISBN 9789781601157.