kara

Daga Wiktionary
Jump to navigation Jump to search

Kara (jam'i: Karare) ana samun kara ne daga jikin shukan Masara ko Dawa ko Gero. anayin katangan kara, ko Rumbu ko Alkalami da shi, kuma ana konawa a wajen yin girki, kuma yara nayin Dokin kara da shi.


Kara ma'ana ta biyu. Wani kebantaccen guri ne a kasuwa da ake sayar da dabbobi, kamar shanu, awaki, tumaki da jakuna.

Kara ma'ana ta uku. Wani yanayi ne da ake yiwa mutum kawaici akan wani abu na rashin jin dadi ba tare da an nuna damuwa akan abin ba a fili.